Revelation of John 19

1Bayan wadannan abubuwa na ji wata karar da ta yi kamar muryar mutane masu yawa a sama suna cewa, “Halleluya. Ceto, daukaka da iko sun tabbata ga Allahnmu. 2Hukunce - hukuncensa gaskiya ne da adalci, domin ya hukunta babbar karuwan nan wadda ta kazamtar da duniya da fasikancinta. Ya dauki fansar jinin bayinsa, wadda ita da kanta ta zubar.”

3Suka yi magana a karo na biyu: “Halleluya! Hayaki na tasowa daga wurinta har abada abadin.” 4Dattawan nan ashirin da hudu da rayayyun halittun nan hudu, suka fadi suka yi wa Allah sujada shi da yake zaune a kan kursiyin. Suna cewa, “Amin. Halleluya!”

5Sai wata murya ta fito daga kursiyin tana cewa, “Ku yabi Allahnmu, dukanku bayinsa, ku da kuke tsoronsa, da duk marasa iko da masu iko.”

6Sai na ji murya kamar na kasaitaccen taron mutane, kamar rurin kogi na ruwaye masu yawa, kuma kamar tsawar aradu, cewa, “Halleluya! Gama Ubangiji yana mulki, Allah mai iko duka.

7Bari mu yi murna, mu yi farinciki matuka mu kuma ba shi daukaka domin bikin auren Dan Ragon ya zo, amaryarsa kuma ta shirya kanta. 8An yardar mata ta sa kaya masu haske da tsabta na lilin mai laushi” (domin lilin mai laushi shine ayyukan adalci na tsarkaka).

9Mala’ika ya ce mani, “Rubuta wannan: Masu albarka ne wadanda aka gayyace su zuwa bikin auren Dan Ragon.” Ya kuma ce mani, “Wadannan kalmomin Allah na gaskiya ne.” 10Na fadi a gaban kafafunsa domin in yi masa sujada, amma ya ce mani, “Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne tare da kai da ‘yan’uwanka wadanda ke rike da shaida game da Yesu. Yi wa Allah sujada, domin shaida game da Yesu shine ruhun annabci.”

11Sai na ga sama a bude, na kuma duba sai ga wani farin doki. Mahayinsa ana kiransa amintacce da gaskiya. Yana shari’a da adalci yana yaki. 12Idanunsa kamar harshen wuta suke, a kansa akwai kambuna da yawa. Yana da suna a rubuce a jikinsa wanda ba wani da ya sani sai dai shi da kansa. 13Yana sanye da riga da aka tsoma a cikin jini, kuma ana kiran sunansa Kalmar Allah.

14Rundunonin sama suna biye da shi a kan fararen dawakai, suna sanye da lilin mai laushi, fari mai tsabta. 15Daga cikin bakinsa takobi mai kaifi na fitowa, da ita yake sarar al’ummai, zai kuma mulke su da sandar karfe. Yana tattake wurin matsar ruwan inabi da matsananciyar fushin Allah Mai iko duka. 16Yana da suna a rubuce a rigarsa da cinyarsa: “Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji.”

17Na ga mala’ika tsaye a rana. Yayi kira da murya mai karfi ga dukan tsuntsaye da ke firiya a sama. 18“Ku zo, ku tattaru saboda babban bukin Allah. Ku zo ku ci naman sarakuna, da naman sarakunan yaki, da naman manyan mutane, da naman dawakai, da na mahayansu, da naman dukan mutane, yantattu da bayi, marasa iko da masu iko.”

19Na ga dabban da sarakunan duniya da rundunoninsu. Suna tattaruwa domin su yi yaki da wanda ke bisa doki da rundunarsa. 20Aka kama dabban tare da makaryatan annabawa da suka yi ayyukan al’ajibai a gabansa. Da wadannan alamu ya yaudari wadanda suka karbi alamar dabbar da wadanda suka yi wa siffarta sujada. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin farar wuta mai ci.

Sauran aka karkashe su da takobin da ke fitowa daga bakin mahayin dokin. Dukan tsuntsaye suka ci gawarwakinsu.

21

Copyright information for HauULB